Sign in
Download Opera News App

News Politics

 

Politics

 

Nigeria politics

Babban Hafsan Sojojin Kasa Ya Kai Ziyarar Gani Ido A Jihonin Ebonyi Da Anambra

Bayan ƙaddamar da Atisayen GOLDEN DAWN, ENDURING PEACE da STILL WATER ranar Litinin 4 ga Oktoba 2021 a Emene da ke jihar Enugu. Babban hafsan sojojin ƙasan Najeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya ya fara ziyarar gani da ido a yankunan da rundunar ke gudanar da Atisayen a jihohin Ebonyi da Anambra.

Janar Yahaya ya fara kai ziyara ne runduna ta 24 ta Injiniyoyin soji da ke Abakaliki in da kwamandan rundunar ya yi taƙaitaccen bayani kan ayyukan rundunar. Tun da farko, babban hafsan ya umarci hafsoshi da ƙananan sojojin rundunar da su nuna ƙwarewa wajen gudanar da ayyukan su, ya kuma yi alƙawarin taimaka ma su domin gudanar da aiki cikin sauƙi. 

Babban hafsan ya kai ziyarar ban girma zuwa ga mai girma Gwamnan jihar Ebonyi, Engineer Dave Umahi. Gwamnan ya yabawa babban hafsan bisa ƙoƙarin sa na magance rikice rikicen kudu maso gabas. Babban hafsan ya godewa Gwamnan da kuma Gwamnonin kudu maso gabas domin ƙoƙarin su na tabbatar da samar da zaman lafiya a yankin. 

Daga nan tawagar ta zarce zuwa jihar Anambra in da rundunar yanki na 5, wadda ta ƙunshi rundunan Manƴan Bidigogi ta 302 da runduna ta 14 ta Injiniyoyin Fili ke gudanar da Atisayen. Kwamandan rundunar Col Abdulkareem Usman ya bayar da taƙaitaccen bayani kan Atisayen a yankin. 

Babban hafsan ya nuna gamsuwar sa da ayyukan rundunar. Ya kuma yaba da irin haɗin kai da ke tsakanin rundunar da hukumomin tsaro na yankin. Ya kuma yi kira ga dakarun da su fuskanci Atisayen kamar yadda aka tsara domin magance tashin hankali da, hana laifuffuka a yankin kudu maso gabas da Najeriya. Ya kuma hore su da cewa rundunar ba za ta yarda da rashin ɗa'a ba. 


BIRGEDIYA JANAR ONYEMA NWACHUKWU 

DARAKTAN HULƊA DA JAMA'A NA RUNDUNAR SOJOJIN ƘASAN NAJERIYA 

5 OKTOBA 2021

Content created and supplied by: NigerianArmyHQ (via Opera News )

Babban Hafsan Bayan Dave Umahi Janar Yahaya Sojojin Kasa Ya Kai

COMMENTS

Load app to read more comments